Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙasa a Nijeriya na ci gaba da raguwa karo na takwas a jere a watan Nuwamba, lamarin da ya samo asali daga raguwar hauhawar farashin abinci a sassan ƙasar.
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS ce ta bayyana hakan a sabbin alkaluman da ta fitar, inda ta nuna cewa matsin lamba kan farashi ya ragu idan aka kwatanta da watannin da suka gabata.
Raguwar ta kai kaso 1.6 idan aka gwada da watan da ya gabata, abin da ke nuna sauƙin hauhawar farashi a tattalin arzikin ƙasar bayan dogon lokaci na tsananin hauhawar farashi.
Karanta: Hauhawar farashin kaya a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 24.23 – NBS
A cewar bayanan da ta fitar a baya bayan nan, hauhawar farashin kayayyakin masarufi ta tsaya a kashi 14.45 a shekara-shekara a watan Nuwamba, sauka daga kashi 16.05 da aka samu a watan Oktoba.
Raguwar hauhawar farashin a wannan shekara ta biyo bayan shekarun da farashi ya yi tashin gwauron zabo, wanda ya jefa rayuwar jama’a cikin tsadar rayuwa a Nijeriya mai yawan al’umma.
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS ta bayyana cewa hauhawar farashi ya kai kusan kashi 35 a watan Disamba na bara, kafin ya fara raguwa bayan da aka sabunta shekarar tushe da kuma daidaita nauyin kayayyaki a ma’aunin lissafin farashi, yayin da babban bankin ƙasa CBN ya nuna burinsa na ganin hauhawar farashi ya ci gaba da raguwa.












































