Darakta janar ta Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya WTao Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, za ta gabatar da laccar kafin bikin yaye dalibai na karo na 45 a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa laccar kafin bikin yaye daliban za ta gudana a jami’ar Ahmadu Bello, inda tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo zai jagoranci taron a matsayin shugaba.
Dakta Ngozi Okonjo-Iweala ta taba rike mukamin ministar kuɗi ta Najeriya sau biyu, daga baya kuma ta rike mukamin ministar harkokin waje na riƙo, inda ta zama mace ta farko da ta rike waɗannan manyan mukamai a tarihin ƙasar.
A lokacin zamanta na farko a matsayin ministar kuɗi, ta jagoranci tattaunawa da ƙungiyar Paris Club wanda ya kai ga goge bashin Najeriya da ya kai Dala Biliyan Talatin, ciki har da soke bashin Dala Biliyan Goma Sha Takwas gaba ɗaya.
Laccar kafin bikin yaye daliban wani ɓangare ne na shirye-shiryen bikin yaye dalibai karo na 45, wanda zai gudana a harabar jami’ar Ahmadu Bello ta Samaru a Zariya, tare da halartar manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar.
Ana sa ran Sarkin jami’ar, Mai Martaba Nnaemeka Alfred Ugochukwu Achebe, Sarkin Onitsha, da kuma Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, za su halarci laccar, tare da shugabannin jami’o’i daga jami’o’in gwamnati da masu zaman kansu.
Shugaban jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Adamu Ahmed, ya bayyana cewa shirye-shiryen bikin sun yi nisa, inda ya gayyaci al’umma gaba ɗaya, shugabannin masana’antu, bankuna, da ƙwararru daga fannoni daban-daban da su halarci laccar da kuma bikin yaye daliban.













































