Wata babbar kotu a Abuja ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar beli da tsohon ministan ƙwadago da aikin yi, Dakta Chris Ngige, ya shigar, inda kotun ta umarci ya ci gaba da zama a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar Alhamis.
Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Maryam Hassan, ta bayar da umarnin tsare Ngige bayan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Tarayya ta EFCC ta gurfanar da shi da tuhume-tuhume takwas na aikata cin hanci da rashawa da ya kai Naira biliyan 2.2.
Hukumar EFCC ta zargi tsohon ministan da bai wa abokan hulɗarsa kwangiloli ba bisa ƙa’ida ba, abin da ya saɓa wa sashe na 19 na dokar hana cin hanci da rashawa ta shekarar 2000, tare da wasu tuhume-tuhume na karɓar rashawa da suka saɓa wa sashe na 17 na dokar.
Dakta Ngige ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa, inda aka tunatar da kotu cewa ya taba zama gwamnan jihar Anambra a ƙarƙashin jam’iyyar PDP daga shekarar 2003 zuwa 2006, sannan ya yi aiki a matsayin ministan ƙwadago daga shekarar 2015 zuwa 2023 a zamanin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Karin labari: Zargin cin Hancin Biliyan 2.2: Kotu ta tsare Ngige a gidan yari,har sai ya cika sharadin beli
A zaman sauraron buƙatar belin, lauyan EFCC ya bayyana wa kotu cewa Ngige na iya tserewa daga ƙasar, yana mai jaddada cewa ya karya sharuɗɗan belin gudanarwa da aka ba shi, musamman dangane da batun fasfo ɗinsa na tafiya ƙasashen waje.
Lauyan Ngige kuwa ya buƙaci kotu da ta ba shi beli, yana mai cewa ba zai iya tserewa ba, yana kuma jaddada cewa ya riga ya sanar da ‘yan sanda game da bacewar fasfo ɗinsa, tare da nuna cewa ba shi da tarihin aikata laifi a baya kuma ba zai iya lalata shaidu ba.
Bayan sauraron dukkan hujjojin bangarorin biyu, Mai shari’a Hassana ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar belin zuwa ranar Alhamis, tare da umarnin a ci gaba da tsare Ngige a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa lokacin yanke hukuncin.
NAN.













































