Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya ce zai kawo karshen shigo da ta tatcen man fetur daga kasashen waje zuwa watan Disamba na shekarar 2024 domin duk matatun man kasar za su fara aiki a lokacin.
An kuma yi hasashen cewa kamfanin mai na kasa zai bunkasa kudaden shiga zuwa N4.5tn a karshen shekarar 2023 inda ya kara da cewa za a kammala aikin gyaran kamfanin matatar mai na Port Harcourt a karkashin jagorancin NNPC a watan Disamba na wannan shekara.
Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a lokacin da ya jagoranci jami’an kamfanin zuwa wata ganawa da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, inda dan majalisar ya bukaci a mayar da matatun man Najeriya zuwa wani kamfani.