Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ta sanar da korar tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Alhaji Shehu Musa Gabam, da shugaban matasa na ƙasa, Ogbonna Chukwuma Uchechukwu, bisa zargin aikata rashin da’a, satar kuɗi da kuma amfani da ofishi ba bisa ƙa’ida ba.
An yanke wannan hukunci ne a taron kwamitin aiki na ƙasa na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, bayan watanni da dama na bincike da kuma zaman kwamitin ladabtarwa.
Mai magana da yawun jam’iyyar, Rufus Aiyenigba, ya bayyana cewa kwamitin ya amince da rahoton da aka gabatar daga kwamitin ladabtarwa da kuma wata takardar mai taken “White Paper” wadda ta ƙunshi shawarwari kan hukuncin da ya dace da wadanda ake zargi.
A cewar Aiyenigba, jam’iyyar ta dakatar da Gabam, Uchechukwu da mai binciken kuɗi na ƙasa, Mista Clarkson Nnadi, tun a ranar 24 ga Yuni, 2025, bayan gano hujjojin da suka nuna akwai almundahana da cin hanci a cikin gudanarwar su.
A cewar sa, daga baya aka kafa wani kwamiti mai zaman kansa a ranar 4 ga Yuli, wanda ya kammala bincikensa a ranar 18 ga Yuli.
Rahoton ya bayyana cewa NWC ta amince da sakamakon binciken a ranar 15 ga Agusta, 2025, wanda ya kai ga korar Gabam da Uchechukwu daga jam’iyyar, yayin da Nnadi ya yi murabus daga mukaminsa.
Jam’iyyar ta kuma kori wasu mambobi takwas saboda rashin biyayya da kuma kutsawa cikin sakatariyar jam’iyyar ba tare da izini ba, inda aka ce jami’an tsaro sun kama su da takardu da wasu kayayyakin jam’iyyar.
SDP ta ce wannan mataki na kora ya zama dole domin dawo da gaskiya, tsari da kuma mutunci a cikin jam’iyyar.













































