Karancin sabon kudi ka iya shafar babban zabe mai zuwa- INEC

INEC Yakubu
INEC Yakubu

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce karancin sabon kudi ka iya shafar gudanar da babban zabe mai zuwa, wanda ya rage saura kwana goma a fara.

Kwamishinan hukumar, Alhaji Yahaya Bello, ya tabbatar da cewa tsarin babban bankin Najeriya CBN, ba makawa zai shafi gudanar da zabe.

Bello ya bayyana hakan ne a wajan taron North-Central stakeholders’ roundtable wanda ya gudana a Abuja ranar Talata.

Ya kara da cewa INEC na bukatar takardar kudin Naira domin ta sami damar biya direbobi da jami’an tsaron da zasuyi aiki a yayin zaben mai zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here