Gwamnatin tarayya ta amince da samar da karin jami’a a jihar Kano

National Universities Commision NUC
National Universities Commision NUC

Gwamnatin tarayya ta amince daga likafar kwaleji zuwa jami’a a kano.

Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta amince tare da daga likafar Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso zuwa Jami’ar Ilimi.

Sakataren zartarwa na hukumar NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, ya mika wa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano takaddar a Abuja.

Sakataren zartarwar ya ce jami’ar ita ce ta 61 mallakar gwamnati kuma ta 221 a daukacin tsarin jami’o’in Najeriya.

Sakataren zartarwar ya yabawa gwamnan bisa wannan shiri na kafa jami’ar, inda ya ce makarantar za ta bada dama wajen biyan bukatun ilimi a jihar.

Tun da farko, Ganduje ya ce sabuwar jami’ar wadda ita ce ta uku da gwamnatin Kano ta mallaka, gwamnatinsa ce ta samar da ita domin biyan bukatu na ilimi da ake samu a jihar tare da samar da ma’aikata masu yawa.

Ya ce, tuni makarantar ta riga tayi karin girma ga malamai 116 da ke da digiri na uku.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here