
Gwamnatin jihar Kano ta umurci majalisar masarautar Bichi da ta dakatar da bikin nadin sarautar Salisu Ado Bayero a matsayin hakimin masarautar.
Jaridar DCL Hausa ta rawaito cewa gwamnatin ta dakatar da nadin na Salisu Ado Bayero wanda kani ne ga Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero.
Karin Labari: ‘Yan bindiga sun sace mutane a wani masallaci a jihar Zamfara
A ranar 15 ga watan Fabrairu ne Masarautar Bichi ta rubutawa Salisu Ado Bayero wasika inda ta sanar da shi amincewar sarkin na a nada shi a matsayin hakimin gundumar Bichi.












































