Wani hatsarin kwale-kwale ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 27 a yankin Gbajibo da ke karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.
Lamarin dai ya faru ne watanni bakwai bayan wani lamari makamancin haka ya lashe rayukan mutane 100 a yankin.
An gano cewa jirgin na dauke da fasinjoji ne da ke dawowa daga wata kasuwa a jihar Neja a lokacin da ya kife.
Wani da ya shaida lamarin kuma wanda ya tsira da ransa ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da daddare a lokacin da suke dawowa daga jihar Neja, kuma kwale-kwalen ya kife ne saboda yawan lodin da ya yi.
Ko da yake ya kasa tabbatar da adadin fasinjojin da ke cikin jirgin, ya kara da cewa iska mai karfi daga guguwar da ke gabatowa ita ma ta taimaka wajen faruwar lamarin.
Karin karatu: Jihar Kwara ta rufe makarantun sakandire 2 saboda rikicin dalibai
Shugaban karamar hukumar Kaiama, Abdullah Danladi, wanda ya jagoranci tawagar gwamnati domin jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya shafa, ya bayyana cewa gwamnati ba za ta sake lamunta da faruwar irin wadannan masifu ba a kusan shekara.
Ya kuma bayyana shirin kafa wani kwamiti da zai tilasta yin amfani da rigunan kare rayuka, da hana zirga-zirgar dare, da aiwatar da wasu matakan tsaro.
Mai martaba Sarkin Kaiama, Alhaji Muazu Umar, ya bayyana cewa za a kara wayar da kan jama’a domin tabbatar da cewa fasinjoji da ma’aikatan jirgin ruwa sun bi ka’idojin kiyaye tafiye-tafiyen ruwa.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata, akalla mutane 60 akasari mata da kananan yara ne suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale a yankin Gbajibo dake kan iyaka tsakanin jihohin Kwara da Neja.
Jirgin ruwan katako da aka kera a cikin gida, mai karfin daukar fasinjoji 100, yana dauke da mutane kusan 300 a lokacin da ya kife.
Kwanaki biyu da faruwar wannan mummunan lamari, shugaban kasa Bola Tinubu ya jajanta wa wadanda hadarin jirgin ruwa ya rutsa da su, ya kuma jajanta wa iyalansu.
Ya umurci hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa NIWA da ta binciki yawaitar hadurran kwale-kwale a Nijar da ma fadin kasar tare da samar da hanyoyin da za a bi domin duba lamarin.













































