Jihar Kwara ta rufe makarantun sakandire 2 saboda rikicin dalibai

Abdulrahman Razak

Gwamnatin jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantar sakandaren gwamnati da na makarantar kwana na gwamnati da ke Adeta, Ilorin, biyo bayan tashe-tashen hankula da dalibai suka fuskanta.

Wannan matakin ya biyo bayan tashe-tashen hankula tsakanin dalibai, da ke barazana ga harkokin ilimi, da barnatar da dukiyoyin makarantu a cikin cibiyoyin biyu.

Da yake tabbatar da rufewar a ranar Laraba, Kwamishinan Ilimi da Raya Jari na Jihar, Dakta Lawal Olohungbebe, ya ce matakin ya zama dole don dawo da zaman lafiya da kuma tabbatar da tsaro.

Ya bayyana cewa daliban da a halin yanzu suke zana jarabawar kammala Sakandare (SSSCE) da malamansu ne kadai za a ba su izinin shiga harabar makarantar a lokacin jarrabawar.

Olohungbebe ya ci gaba da ba da umarnin cewa duk masu neman shiga SSSCE dole ne su sanya katin shaidar makarantar su domin shiga harabar.

Karin karatu: Tinubu zai kafa rundunar masu tsaron dazuka a faɗin Najeriya

Ya kuma bukaci iyaye da masu kula da su, da su tabbatar da ‘ya’yansu sun zauna a gida, yana mai gargadin cewa duk dalibin da aka samu ya saba dokar jami’an tsaro za su kama shi.

Gwamnati ta jaddada kudirinta na kiyaye da’a da tsaro a duk makarantun gwamnati a jihar. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here