An gano wata yarinya mai shekara 13 a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, wadda ta bace kimanin makonni biyu da suka gabata a Jihar Kaduna.
Bayanai sun ce an gano yarinyar ce yayin da take sintiri a titi ba tare da sanin ina ta dosa ba, dalilin ke nan na kama ta kuma aka mika wa ’yan sandan yankin.
Da yake jawabi yayin mika yarinyar ga iyayenta a ranar Alhamis, mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Borno, ASP Sani Kamilu, ya ce sun yin bincike mai zurfi kafin gano iyayen yarinyar.
Ya ce, “Ta kasance karkashin kulawar CSP Hadiza Musa Sani wanda a ofishinta aka fara gabatar da batun mako biyu da suka shige.”













































