Gwamna Babagana Zulum na Borno ya rattaba hannu kan wasu umarni biyu wadanda za su hana sare bishiyoyi da kuma ba da umarnin gudanar da aikin tsaftace muhalli a duk wata a fadin jihar.
A ranar Asabar ne aka sanya hannu kan wannan umarnin a gidan gwamnati da ke Maiduguri.
Umarnin sun kasance wani bangare na kokarin magance lalata muhalli da inganta lafiyar jama’a a fadin jihar.
Zulum ya ce matakin ya mayar da martani ne ga mummunan cin zarafi, musamman yankan itatuwa ba bisa ba, wanda ke barazana ga muhalli.
Karanta: Hukumar tace fina-finai ta haramta bikin ƙauyawa a jihar Kano
Ya bayar da misali da cewa umarnin na karkashin sashe na 14 (2) da na 20 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, wadanda aka yi wa kwaskwarima, a matsayin ginshikin matakin zartarwa.
Wadanda suka karya doka za su fuskanci tarar Naira 250,000 ko kuma daurin shekaru uku a gidan yari saboda laifin farko.
Idan kuma mutum ya maimaita laifin zai fuskanci tarar Nsira 500,000 ko daurin shekaru biyar.
Dokar zartarwa ta biyu ta ayyana ranar Asabar ta farko na kowane wata a matsayin ranar tsaftar mahalli, da nufin inganta tsafta da rigakafin cututtuka a tsakanin al’ummar jihar Borno.
A cewar gwamnan, wadanda suka karya wannan umarni na iya biyan tarar Naira 100,000 ko kuma su fuskanci hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari kan laifin farko.
Maimaita laifin na iya fuskantar daurin shekaru biyar a gidan yari, Zulum ya yi gargadin, yana mai jaddada muhimmancin umarnin.
Gwamnan ya kuma bai wa kotun kula da tsaftar muhalli ikon aiwatar da dokar zartaswa yadda ya kamata a fadin jihar.
Zulum ya umurci rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar da su tabbatar da bin dukkan umarnin zartarwa. (NAN)













































