Yayan Malam Ibrahim Shekarau, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Dahiru Shekarau, ya rasu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon gwamnan, Farfesa Sule Yau Sule, ya fitar a ranar Laraba ta ce Dahiru Shekarau ya rasu a wani asibiti mai zaman kansa a ranar Talata bayan jinya mai tsawo.
SolaceBase ta ruwaito cewa za a yi sallar jana’izar mamacin, wanda ya kasance tsohon Babban Sakatare a Ma’aikatar Gwamnatin Jihar Kano, a Masallacin Juma’a na Giginyu da ke karamar hukumar Nasarawa da karfe 10:00 na safiyar yau, Laraba.












































