Daurawa ya sauka daga shugabancin hukumar Hisbah a Kano

Screenshot 20240301 094842 WhatsAppBusiness

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi murabus daga muƙaminsa na shugaban hukumar Hisbah a jihar.

Murabus ɗin malamin na zuwa kwana guda bayan da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan salon da hukumar Hisbah ke bi wajen yaƙi da masu aikata baɗala a Kano.

A wani bidiyo mai tsawon ƙasa da minti uku da Sheikh Daurawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya bayyana cewa kalaman gwamnan sun kashe masa gwiwa kuma a don haka ya ajiye muƙaminsa na jagora a hukumar ta Hisbah.

Daurawa ya ce “Mun yi iya ƙoƙarinmu domin yin abin da ya kamata, to amma ina bai wa mai girma gwamna haƙuri bisa fushi da ya yi da maganganu da ya faɗa. Kuma ina roƙon ya yi mani afuwa na sauka daga wannan muƙami da ya bani na shugabancin Hisbah.”

A ƴan kwanakin da suka gabata ne, Hisbah ta kama shahararriyar ƴar tiktok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya bisa zargin aikata baɗala a jihar Kano lamarin da hukumar ta ce ke lalata tarbiyyar matasa.

Hukumar ta kuma aika ta zuwa kotu wadda kuma ta tura ta gidan gyaran hali.

Bayan an aika ta gidan gyaran hali ne kuma aka wayi gari da labarin sakinta daga kurkuku, abin da ya yi ta tayar da ƙura a tsakanin al’ummar jihar inda wasu ke ganin da hannun gwamnati a sakin nata – zargin da gwamnatin ta musanta.

A yanzu dai Murja Kunya na asibitin masu larurar ƙwaƙwalwa bisa umarnin kotu domin gwada lafiyar ƙwaƙwalwarta. Kotun ta ce ƴar Tiktok ɗin za ta yi wata uku a can.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here