Tirela Ta Kutsa Cikin Masallaci Ana tsaka Da Sallar Asuba

Truck accident
Truck accident

Wata Tirela dauke da madarar foda ta kutsa cikin wani masallaci da ke Suleja a jihar Neja a ranar Talata, inda akalla mutane uku suka makale.

Hadarin ya afku ne da misalin karfe 6 na safe inda mutane da dama suka bar masallacin bayan sallar asuba.

Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, tirelar ta afka ne a sashin baya na masallacin da mata da kananan yara ke sallah.

Sai dai mutane uku ciki har da wani yaro guda sun makale a cikin kango inda daga bisani suka samu raunuka.

A lokacin da Aminiya ta ziyarci wurin, an ga wasu jama’a a kusa da motar da ta fado wadda ta tare wani bangare na titin Bida da ke kusa da babbar kasuwar Babangida.

Rahotanni sun ce motar tirelar ta fadi ne a lokacin da take kokarin wuce wani lungun hanyar da aka zuba tulin yashi da ake amfani da shi domin gina sabbin shaguna.

Wani mazaunin garin Baba Maiunguwa wanda ya zanta da wakilinmu ya ce an kai mutane uku babban asibitin Suleja domin yi musu magani.

Ya ce, “Hatsarin ya faru ne bayan Sallar Asuba. An kai mutane uku asibiti ciki har da wani yaro. Alhamdulillah babu mutuwa.

“Mun yi sa’a, mutane sun fita daga Masallaci bayan an yi Sallah. Da abun yi muni, da gurin acike yake a lokacin Sallah”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here