Gwamnatin Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya ta sanar da hana fitar da kayan abinci domin shawo kan tsadar rayuwa da kuma hauhawar farashin da ake fuskanta a jihar.
Gwamnatocin jihohi da dama a arewacin Najeriya sun dauki irin wannan mataki, don tabbatar da wadatar kayan abinci a cikin kasar.
Karanta wannan: Majalisar dattawa za ta binciki Emefiele da tsohuwar gwamnatin Buhari
A nata bangaren, gwamnatin Najeriya ta haramta fitar da kayan abinci zuwa wasu kasashe da ke makwabtaka da ita, inda ko a farkon makon nan sai da aka kama motoci 50 dauke da kayan abinci a jihar Zamfara a kokarin ketawa da su Jamhuriyar Nijar.
Al’umma da dama a Najeriya na ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwar da ake fama da shi a kasar.