Majalisar dattawa za ta binciki Emefiele da tsohuwar gwamnatin Buhari

Buhari, Emefiele,bincike, kudi, EFCC, dala, miliyan
An ci gaba da shari'ar da ake yi wa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda aka tabbatarwa kotu cewa binciken kimiyya ya...

Majalisar Dattawar Najeriya ta tsaida shawarar gudanar da bincike a kan yadda tshohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi amfani da basukan Naira Tiriliyan 30 da ta karbo daga babban bankin kasar.

Gwamnatin Buhari ta yi amfani da tsarin da babban bankin kasar ya kira ‘Ways and Means’ ne, inda ake samar mata da kudaden toshe gibin da aka samu a kasasfin kudinta.

Majalisar Dattawar ta ce yadda aka kashe wadannan kudaden da aka karbo daga babban bankin a karkashin jagorancin Emefiele ba bisa ka’ida ba ne ummul’aba’isin matsalar abinci da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

Karanta wannan: DSS ta gargaɗi NLC kan ƙudurinta na shirya zanga-zanga

Saboda haka ne majalisar ta yanke shawarar kafa wani kwamitin da zai gudanar da bincike a kan yadda gwamnatin Buhari ta kashe naira  tiriliyan 30 din, tana mai nuni da cewa da gangan aka ki baiwa majalisar dokokin kasar bayani a kan yadda aka kashe kudaden.

Kwamitin, wanda a Larabar nan za’a kaddamar da shi, zai kuma binciki yadda aka bada bashin naira biliyan 10 a karkashin shirin rancen manoma na Anchor Borrowers, da kuma hada-hadar kudaden musanya na kasashen waje da ya kai dala biliyan 2 da miliyan dari 4.

Karanta wannan: IGP ya gargadi rundunar ‘Yan Sandan Najeriya

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsadar abinci da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kuma faduwar darajar naira da matsalar tsaro ke ci gaba da ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da tawagar tattalin arzikinsa sun sha caccaka bayan da janye tallafin man fetur da ya yi, tare da mayar da tsarin canjin kudaden musanya na bai daya suka jefa al’ummar kasar cikin matsanancin kuncin rayuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here