Dangane da yadda jama’a ke kara nuna damuwa kan yadda ake sayar da abinci a yanayi na rashin tsafta, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da wani gagarumin aiki magance matsalar sayar da abinci s gefen titina.
SolaceBase ta rawaito cewa, aikin hadin gwiwar hukumomin gwamnati da dama ne, kuma an yi ne da nufin kare lafiyar jama’a da kiyaye ka’idojin muhalli.

A ranar Larabar da ta gabata ne, tawagar da kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Dakta Dahir M. Hashim ya jagoranta, ta gudanar da bincike a wurare da dama da suka shahara wajen rashin tsafta kuma ana sayar da abinci, da suka haɗa da Naibawa, da tashar Motar ta Kano line da Titin BUK.
A yayin ziyarar, Dakta Hashim, ya yi karin haske kan yanayin da ake ciki a Naibawa Yan Lemo, inda tawagar ta gano cewa ana bahaya a fili duk da cewa ana sayar da ‘ya’yan itace.

“An dauki matakin gaggawa kuma mun ba da umarnin kwashe duk kayan abinci da ke wurin kuma mun ba da umarnin a tsaftace wurin sosai, an tura jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA domin tabbatar da bin wannan umarni.”
Labari mai alaƙa: Gwamnatin Kano ta samar da dokar kare muhalli don yaƙi da gurɓatar yanayi
A tashar mota ta Kano line da Titin BUK, an gano masu sayar da kayayyaki masu lalacewa irin su madara da kifi cikin rashin tsafta a gefen titi. A cewar Dakta Hashim, irin wadannan ayyuka ba wai kawai suna kawo hadari ga lafiyar jama’a ba ne, har ma suna haifar da cunkoson ababen hawa.

Dakta Hashim ya jaddada cewa, wannan aiki ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da tsaftataccen muhalli ga daukacin mazauna jihar Kano. Ya kuma jaddada muhimmancin kiyaye tsaftar muhalli wajen sarrafa abinci da sayar da shi domin hana barkewar cututtuka.
Tawagar duban wuraren sun hada da Manajan Daraktan KAROTA, Engr. Faisal Mahmud, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ibrahim Adam, daraktoci daga ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, da wakilai daga hukumar kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta jihar Kano (KSCPC).













































