Ghana na zargin ‘yan siyasa da sarakuna kan ayyukan masu hakar ma’adanai

Ghana, sarakuna, 'yan siyasa, hakar, ma'adanai,
Hukumar kula da gandun daji a Ghana ta zargi 'yan siyasa da sarakunan gargajiya da hura wutar yawaitar masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da ake kira da...

Hukumar kula da gandun daji a Ghana ta zargi ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya da hura wutar yawaitar masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da ake kira da “Galamsey” a dazukan kasar.

Jaridar Daily Graphic da ke kasar ta rawaito cewa, a halin yanzu ayyukan masu hakar ma’adanan sun gurbata dazukan kasar, duk da kokarin da hukumar ke yi akan dakile wannan matsalar.

Karin labari: NLC ta jaddada shirin gudanar da zanga-zanga duk da barazanar DSS

Ma’aikatan gandun dajin kasar sun damu matuka, kan yadda suke sadaukar da rayuwarsu wurin kama irin wadannan masu hakar ma’adanai, amma daga bisani ‘yan siyasa da sarakuna su yi amfani da karfinsu wurin kubutar da su ba tare da barin doka ta yi aiki akansu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here