Daga Abdulkadir Ahmed
Inna Lillahi Wa’inna Ilaihir’raji’un. Tare da mika wuya ga Allah (SWT) a madadin ‘Yan uwa da abokan aikina na wannan zamani Ina sanar da rasuwar babban abokina kuma masoyi, amintacce kuma abin koyi, gogaggen dan jarida, Alhaji Abdulhamid Babatunde Agaka, FNGE.
Marigayin ya rasu ne da sanyin safiyar Alhamis 28 ga watan Yuli, 2022, a gidansa da ke Malali, a Jihar Kaduna, inda aka gudanar da sallar jana’izar sa da safe, sannan aka binne shi a makabartar al’ummar yankin.
Idan za a iya tunawa, gogaggen dan jaridar kuma mai ba da shawara kan harkokin yada labarai, ya yi rashin matarsa ta farko, Salamatu Babatunde, a watan da ya gabata na Yuni.
An haifi Abdulhamid Babatunde Agaka a ranar 26 ga Fabrairu, 1956, ya halarci makarantar Kano Capital da kuma Capital School Kaduna a shekarun 1960 kafin ya wuce zuwa Kwalejin Barewa Zariya da Makarantar Sakandare ta Gwamnati a Ilorin babban birnin Jihar Kwara.
Marigayin tun tasowarsa ya kasance Mai sha’awar aikin jarida, ya shiga aikin jarida a Shekarar 1974, inda ya fara aiki a Jaridar New Nigerian da ke Kaduna.
Ya kasance Wakilin Jaridar na Jihar Kano Kuma Editan Jaridar daga shekarar 1980 zuwa 1984.
Hazikin dan jaridar ya yi tasiri sosai wajen samar da ci gaba a bangarorin zamantakewa da tattalin arziki da siyasa da kasuwanci da al’adu da addini tare da rubuta labarai da suka shafi al’umma da al’amuran jihar Kano a wancan lokaci.
An mayar da Abdulhamid Babatunde Jihar Kaduna a karshen 1984 kuma ya koma ne a matsayin Editan Labarai kafin ya daga bisani ya koma Jaridar Democrat itama a matsayin Edita a Shekarar 1988 sannan daga baya ya zama shi ne Babban Editan Jaridar ta Democrat News paper.
Lokacin da jaridar ta daina bugawa a Shekarar 1996, ya fara aikin Media Consultancy inda ya kafa Slim Jenkins Media Services wani kamfani mai ba da shawara kan yadda za a kafa tare da gudanar da kafofin yada labarai, kabar tallace-tallace da bada horo ga Yan Jarida, da kamfanoni.

Abdulhamid Babatunde Agaka, wanda ya halarci horon aikin jarida da bita da tarurruka da dama a gida da waje, tsohon dalibi ne a Cibiyar Aikin Jarida ta Najeriya da ke Legas wadda ya halarci cibiyar tsakanin Shekarar 1976 zuwa 1978.
Ya kasance Mamba a kungiyar ‘yan jarida ta Kasa NUJ reshen Jihar Kano (daga shekarar 1980 zuwa 1984)
Marigayin daga baya ya shiga kungiyar Editoci ta Kasa, wato Nigerian Gilt of Editors, inda ya taba zama mataimakin shugaban kungiyar na yankin Arewa.
Abdulhamid ya samu lambobin yabo da dama, sakamakon jajurcewa da kwazo a kan aikin sa.
Alhaji Abdulhamid, wanda shi ne Sakataren Kwamitin Jokolo da Shugaba Olusegun Obasanjo ya kafa, a shekarar 1999, ya rasu ya bar ‘ya ’ya hudu: Ahmad da Maryam da Halima da Abdulhamid (Junior).
Ya kuma bar sauran ‘yan uwa da suka hada da Malam Ismail Ila Agaka, tsohon Manajan Darakta na Asusun Kula da Inshora na Kasa (NSITF) da Ilyasu Baba Agaka, Darakta a Fadar Shugaban Kasa da dai sauransu.
Allah (S.W.T) ya sa ya huta Ameen!














































