Dakarun haɗin gwiwar sojojin Najeriya da na jami’an DSS sun ce sun yi nasarar daƙile wani hari da wasu ‘yan tayar da ƙayar bayan Boko Haram suka shirya kai wa a Kano da ke arewacin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta wallafa a shafinta an X ta ce, hadin gwiwar jami’an tsaron sun kai wani ƙaramar hukumar Gezawa da ke jihar Kano, da nufin ganowa tare da kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne da ake kyautata zaton suna shirin wani gagarumin farmaki a Kano.
Sanarwar ta ce a lokacin samamen, jami’an tsaron sun kama mutum biyu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne, kuma an ƙwato manyan makamai da ababen fashewa.
“Wannan farmakin ya nuna kyakkyawan hadin gwiwa da ke tsakanin jami’an tsaron da kuma jajircewar sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro na dakile ta’addanci da kuma inganta tsaro a faɗin ƙasar”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Rundunar Sojin ƙasar ta ƙarfafa wa jama’a gwiwa don bayar da muhimman bayanan da za su taimaka wa ƙoƙarin suke yi yi na magance matsalar tsaro a ƙasar.