‘Yan bindiga sun kashe mutun 5, yayin da 4 suka jikkata a wane harin yan bindiga a jihar Sokoto

Nigeria Kidnappings Bandits deputy
Nigeria Kidnappings Bandits deputy

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a garin Duhuwa da ke cikin karamar hukumar Wurno a jihar, inda suka kashe akalla mutane biyar yayin da wasu hudu suka samu raunuka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Ahmad Rufa’i, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an yi awon gaba da wasu da dama.

A halin da ake ciki kuma, wani mazaunin kauyen Dalhatu Duhuwa, bai amince da ‘yan sanda kan adadin wadanda suka mutu ba, wanda ya ce mutum shida ne ba biyar ba kamar yadda ‘yan sanda suka sanar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here