Bai kamata a zargi mijinta ba kan tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya – Oluremi Tinubu

Remi Tinubu 634x430 1

Mai dakin shugaban kasan Nigeria, Oluremi Tinubu ta ce bai kamata a zargi mijinta, Bola Tinubu ba, kan tabarbarewar tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.

‘Yan Najeriya dai na cikin matsin tattalin arziki tun bayan cire tallafin man fetur wanda ya sa farashin man fetur daga N198 zuwa N1,030.

Tinubu ya sanar da kawo karshen tallafin a yayin jawabinsa na kaddamarwa a ranar 29 ga Mayu, 2023, inda ya ce manufar ta kawo cikas ga ci gaban Najeriya.

Sai dai a lokacin da take magana a fadar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, a ranar Alhamis.

Uwargidan shugaban kasar ta je garin Ife ne domin kaddamar da wani titin kilomita 2.7 da Ooni na Ife ya ba Jami’ar Obafemi Awow

“Mun san cewa an cire tallafin, amma da Allah a wajenmu, nan da shekaru biyu masu zuwa, Nijeriya za ta fi haka. Amma da addu’o’in ku nan da shekaru biyu masu zuwa za mu gina al’umma ta gaba”.

Uwargidan shugaban kasar ta kara da cewa mijinta ba mai kwadayi ba ne, tana mai godewa Allah da ya sa ya zama dan kasa na daya a Najeriya.

“Muna godiya ga Allah da matsayinmu, ni da mijina, ba mu da kwadayi amma muna gode wa Allah da abin da Allah Ya yi mana. Ba a saba ganin masu hannu da shuni su hau wannan kujera ba amma ina godiya ga Allah, ba za mu iya ba Najeriya kunya ba kuma da taimakon Allah muna isa kasar alkawari nan ba da dadewa ba,” inji ta.

Uwargidan shugaban kasar wacce ta bayyana cewa ta kammala karatun ta a OAU shekaru 41 da suka gabata ta baiwa jami’ar gudummawar Naira biliyan 1 domin ci gabanta .

Da yake jawabi, Ooni na Ife, ya yabawa uwargidan shugaban kasar bisa yadda ta zama abin koyi ga matasa tun zamanin da take a matsayin uwargidan gwamnan jihar Legas.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here