Wata matar aure ta mutu a Jigawa sakamakon ruftawar gini

Jigawa map
Jigawa map

Wata matar aure ‘yar shekara 45 ta rasu yayin da mijinta ya samu raunuka sakamakon ruftawar gini a karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

Mai magana da yawun hukumar tsaron farin kaya ta Kasar nan NSCDC a jihar, CSC Adamu Shehu, ya tabbatar da faruwar a Dutse ranar Talata.

Shehu ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 11 da mintuna 30 na Safiya, sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a yankin.

Ya ce mijin mai suna Malam Shehu Na’Allah, mai shekaru 60, ya tsallake rijiya da baya, inda ya garzaya asibiti domin kula da lafiyarsa, yayin da matarsa ​​Talatu ta rasu a cikin baraguzan ginin.

Mai magana da yawun hukumar ya kara da cewa yanzu haka an bada gawar marigayiyar ga iyalanta domin yi mata jana’iza bayan wani likita ya tabbatar da mutuwar ta.

A cewarsa, ruwan saman da ya dauki tsawon sa’o’i da dama ya yi sanadiyyar lalata gidajen laka da dama a yankin.

Shehu ya ce jami’an hukumar kula da bala’o’i sun sauyawa mutanen da gidajensu ke gab da rugujewa matsugunnai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here