Kotu ta bayar da umarnin gaggauta sakin Emefiele

Godwin Emefiele
Godwin Emefiele

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ce kamawa tare da tsare dakataccen gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele da DSS ke yi ya saɓa wa doka.

Yayin da yake yanke hukuncin Mai shari’a Bello Kawu ya ce kamawa da kuma bincikar Mista Emefiele, ya saɓa wa hukunci da kuma umarnin da wata kotun ta bayar na sakin sa.

Lauyan Mista Emefiele, Peter Abang, ya nemi kotun da ta jingine sannan ta ayyana kamu tare da tsare shin da hukumar DSS ke yi a matsayin haramtacce.

Kasancewar a ranar 29 ga watan Disamban 2022 wata kotu ta dakatar da kama mista Emefiele.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here