Yanzu Yanzu: Jirgin Rundunar Sojin Sama Ya Yi Hatsari a Benue 

BREAKING 2
BREAKING 2

Wani jirgin saman horar da sojojin saman Najeriya FT-7NI ya yi hatsari a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Daraktan hulda da jama’a da labarai na rundunar NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a. Ya ce matukan jirgin biyu da ke cikin jirgin sun tsira kuma ana kan kula da su a wani asibitin sojoji. Gabkwet ya ce:

“An yi sa’a matukan jirgin biyu sun tsira a hatsarin bayan da suka yi nasarar fita daga jirgin. Bugu da kari, ba a rasa rai ko daya,  ko lalata kaya a yankin da abun ya faru ba. ”

“Yanzu haka dukka matukan jirgin na karkashin kulawa a asibitin sojoji, Makurdi. A halin da ake ciki, shugaban hafsan soji, Air Vice Marshal Hasan Abubakar, ya kafa wani kwamitin bincike don gano abun da ya haddasa hatsarin.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here