Ƙungiyar Direbobin Tankar Mai ta buƙaci direbobi su yi watsi da sanarwar yajin aikin NUPENG

IPMAN Fuel Tankers (1)

Ƙungiyar direbobin Tankar Mai (PTD) ta bukaci mambobinta su yi watsi da sanarwar yajin aikin da Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da iskar Gas (NUPENG) ta bayar.

Tun da farko a ranar Juma’a, NUPENG ta bayyana cewa za ta fara yajin aiki daga 8 ga Satumba, tare da umartar ma’aikata su fara neman wasu ayyuka, tana mai zargin Kamfanin Dangote da hana direbobin motocin iskar gas (CNG) shiga ƙungiyoyin kwadago.

Sai dai a wata sanarwa, PTD ta yi watsi da wannan mataki, tana kiran shi a matsayin “mara tushe” tare da cewa bai dace ba a yanke hukunci ba tare da tattaunawa ko shawarwari da masu ruwa da tsaki ba.

Ƙungiyar ta bayyana cewa duk inda ake da ƙungiya a duniya, shiga cikinta na son rai ne, kuma shirin shigo da motocin CNG 4,000 daga Kamfanin Dangote ya yi don rarraba mai kai tsaye ya dace da muradun jama’a.

Labari mai alaƙa: Ana fargabar ƙarancin Fetur, yayin da NUPENG ke shirin fara yajin Aiki kan matakin Dangote

PTD ta kuma ce dole ne a warware sabani ta hanyar tattaunawa da kyakkyawar alaƙa, ba da barazana ko tashin hankali ba, domin Najeriya tana karkashin tsarin dimokuraɗiyya.

Haka kuma, ƙungiyar ta zargi NUPENG da gazawa wajen kawo zaman lafiya da haɗin kai a harkar man fetur.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here