
Kwamitin majalisar wakilai mai yaki da cin hanci da rashawa ya baiwa Mista Ola Olukoyede, shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC har zuwa ranar 30 ga watan Yuli da ya gurfana a gabanta kan batutuwan kasafin kudi.
Kwamitin ya ce ya kamata Olukoyede, tare da tawagar gudanarwar sa, su fito su amsa tambayoyin da suka shafi kasafin kudin hukumar da kuma kalubalen da ke fuskanta.
Shugaban kwamitin, dan majalisa Obinna Onwusibe, ya bayyana rashin jindadinsa a wani sa’in sa da ofishin hukumar da ke Abuja.
Kwamitin ya yi Allah-wadai da abin da ya bayyana a matsayin halin kakani-kayi na shugaban hukumar da kuma hana mambobin kwamitin shiga harabar hukumar.
Karin labari: An sanya ranar zaben kananan hukumomi a Jigawa
Bayan hana shiga harabar hukumar, ‘yan kwamitin sun dawo suka nufi bas dinsu suka koma majalisar dokokin kasar.
Kwamitin ya ziyarci hedikwatar EFCC ne bayan tattaunawa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa tare da cimma matsaya kan ranar ziyarar sa ido.
Sai dai kuma an shaidawa kwamitin cikin mamaki cewa an kira shugaban da ya yi gaggawar kawo masa dauki a babban bankin Najeriya CBN.
Da yake mayar da martani, shugaban kwamitin ya ce: “A yayin gudanar da ayyukanmu na tsarin mulki mun rubutawa EFCC wannan ziyarar sa ido.
Karin labari: An sanya ranar zaben kananan hukumomi a Jigawa
“Sabuwar wasiƙar zuwa ga EFCC ita ce a makon da ya gabata kuma duk mun amince cewa za a sa ido a yau.
“Dalilin sa idon shi ne, kwamitin ya san yadda hukumar EFCC ke gudanar da kasafin kudin kamar yadda wannan majalisar ta kasa ta tsara.
“Hakan ya sa muka je da kuma ganin wasu abubuwa, ciki har da kalubalen da EFCC ke fuskanta” in ji shi.
Sai dai kwamitin ya yanke shawarar cewa ba za ta ci gaba da sa ido ba kuma ta yanke shawarar kara kiran shugaban hukumar ta EFCC da tawagarsa da su gurfana a gabansa kamar yadda NAN ta bayyana.