Hukumar dake kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta jihar Kogi, ta bada umarnin kama wani jami’inta bisa sakacin sa na salwantar da bindigogi biyu da harshashai masu yawa.
A wata sanarwa da kakin hukumar na jihar, DCS Nihi Sesan, ya fitar, ya sanar da umarnin kama jami’in da gaggawa.
Duk da cewa a sanarwar da hukumar ta fitar ranar Laraba a Abuja, bata ambaci sunan jami’in ba.
Sanarwar ta kara da cewa, an samu nasarar nemu bindigogin da ya salwantar, sanan hukumar na cigaba da buncikin jami’in.












































