Gwamna Zulum Ya Yiwa Almajirin Borno da Ya Kirkiri Taraktan Hannu kyautar N5m

unnamed 2
unnamed 2

Gwamna Babagana Umara Zulum, ranar Laraba, ya bayar da kyautar Naira miliyan biyar (N5m) don tallafawa fasahar wani almajiri mai hazaka a jihar Borno, wanda ya kera injin din garma.

Zulum, wanda farfesa ne a fannin noman ban ruwa, ya ji dadin yadda Laminu Mohammed, dan shekara 25 daga karamar hukumar Gubio da ke arewacin jihar Borno, da bai taba zuwa wata makarantar boko ba sai ilmin addinin Musulunci na gargajiya da ake kira Tsangaya a Borno ya kirkiri Tractan hannu.

Laminu ya yi amfani da abubuwan da ke cikin injin din lister wanda asalinsa an yi shi ne don famfo ruwa, wajen kera garma mai aiki kamar tarakta wanda ake turawa da hannu.

Wani jami’in gwamnati ne ya sanar da Zulum basirar Laminu. Zulum wanda injiniya ne, ya gayyato Laminu, suka tattaunawa game da fasahar, inda almajirin ya nuna kwarewarsa a kan kirkirar da yayi, daganan aka ba shi kyautar N5m.

Gwamnan ya ce kudaden na da nufin zaburar da ‘injiniyan da bai je makarantar boko ba da samar da karin garma da kirkiran wasu injunan noma wanda manoman jihar Borno zasu amfana da shi.

Tallafin Zulum ga Laminu ya zo ne makonni biyu bayan Gwamnan ya amince da sama da N5m ga wani matashi dan shekara 13 da ya yi amfani da laka wajen zana gadar sama ta farko a Borno da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Gamboru Ngala.

A wani labarin kuma, Zulum ya bayar da kyautar kananan motocin bas guda biyar da tsabar kudi N20m ga wani matashi dan jihar Borno da ya kware wajen mayar da motocin bas da injinan mai zuwa motocin lantarki masu amfani da hasken rana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here