Shugaban rukunin kamfanonin BUA Abdulsamad Rabi’u, ya yi watsi da zaben sa a matsayin mamba na kwamitin harkokin kudi na Jam’iyyar APC.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a.
A baya dai APC ta zabi Abdulsamad, a matsayin guda cikin mambobin kwamitin kudi mai mutum 34 da jam’iyyar ta kafa a ranar alhamis.
A cewar kamfanin APC ba ta tuntubi shugaban BUA ba lokacin da ta sanya shi cikin mambobin kwamitin.
Idan za a iya tunawa dai a ranar alhamis ne sakatariyar APC ta tura sunayen mambobin kwamitocin da ta kafa a manhajar Whatsapp.
Sai dai bayan wasu sa’o’I an ga ta goge jerin sunayen mambobin kwamitocin.