Gobara ta kone wani sashe na jami’ar Ahmadu Bello Zaria

ABU Zaria sabo
ABU Zaria sabo

Sashen ginin Majalisar zartarwar jami’ar Ahmadu Bello dake Samaru a Zaria ya kone sakamakon gobara.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya rawaito cewa gaba daya dakin da na’urorin rarraba lantarki suke ya kone.

Daraktan sashen yada labarai na Jami’ar ya tabbatar da aukuwar lamarin ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Sanarwar tace tuni shugaban Jami’ar Farfesa Kabiru Bala, ya halacci wajen da lamarin ya faaru tare da sauran masu ruwa da tsaki.

Kazalika, hukumar jami’ar ta kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here