Sabon tsarin mafi karancin albashi zai fara aiki a watan Aprilu- Gwamnatin tarayya

Bola Tinubu new 720x430
Bola Tinubu new 720x430

Gwamnatin tarayya tace sabon tsarin mafi karancin albashi, zai fara aiki daga watan Aprilun 2024.

Ministan yada labarai, Idris Muhammed, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da

manema labarai a Abuja.

Yace tsarin biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 30 da ake amfani

da shi a halin yanzu zai daina aiki ne a karshen watan Maris din shekara

mai zuwa ta 2024.

Muhammad, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da yake fayyace

taswirar kasafin kudi na shekarar 2024 zuwa 2026 wanda ya nuna cewa

Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira triliyan 24 da biliyan 66 kan albashin

ma’aikata kawai a tsakanin shekarun 2024 da 2025 da kuma 2026.

Tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi a ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata ne, gwamnatin tarayyar ta amince da biyan mafi karancin albashin naira dubu 35 ga ma’aikata.

Tun a ranar 18 ga watan Oktoban 2019 ne tawagar Gwamnatin tarayya da majalisar tattaunawa kan batutuwan da suka shafi ma’aikata ta Kasa, suka amince da aiwatar da mafi karancin albashi na Naira dubu 30, bayan shafe watanni ana tattaunawa.

Sai dai a ranar Alhamis din nan kungiyar kwadago ta tabbatar da cewa sun fara tattaunawa da gwamnatin tarayya, inda suka kara da cewa bisa tsarin dokar kwadagon Najeriya ya kamata a rinka duba mafi karancin albashi duk bayan shekaru biyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here