Kwamishinan ‘Yan sanda ya bada umarnin a kama Jami’in da ya harbi wani ya mutu a Kano

Police badge
Police badge

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammad Usaini Gumel ya bada umarnin cafke wani Sifeta bisa zargin yin aiki cikin rashin kware da hakan ya yi sandiyar mutuwar mutum daya tare da jikkata wasu biyu a jihar.

A wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar ‘Yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Laraba, ta ce rundunar yanzu haka tana bin diddigin lamarin da ya faru tun a ranar 28 ga watan Nuwambar 2023, a Unguwar Kurna dake yankin karamar hukumar Fagge, inda wasu gungun matasa suka yi dauki ba dadi da wani sifeton ‘yan sanda.

A cewar sanarwar a yayin da suke fadan Jami’in bai samu wani umarni daga rundunar ‘yan sanda ba kawai ya yi harbi wanda ya yi sanadiyar raunata mutane biyu tare da wani mutum guda ya mutu bayan kai shi Asibiti.

Karanta: A ci gaba da amfani da sabbi da tsofin kudin har illa masha Allah-Kotun koli

A ci gaba da amfani da tsofin kudi har illa masha Allah-Kotun koli

Sanarwar ta ci gaba da cewa, a halin yanzu kwamishinan ‘yan sandan Jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, FIPMA, psc, ya umarci Kwamandan yankin Dala, ACP Nuhu Mohammed Digi da ya kama sifeton ‘yan sandan tare da kafa kwamitin bincike kan musabbabin faruwar lamarin wanda za a sanar da sakamakonsa ga jama’a.

Yanzu haka an kama sifeton ‘yan sandan kuma yana tsare hannun ‘yan sanda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here