Buhari ya rantsar da sababbin Manyan sakatarorin Gwamnatin Tarayya

newly appoint secretarties
newly appoint secretarties

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin manyan sakatarori hudu ranar Laraba a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa shugaba Buharin ya rantsar da Manyan Sakatarorin ne kafin fara taron Majalisar Zartarwa na tarayya.

Sababbin Sakatarorin hudu sune Uwar gida Beatrice Jiddy-Agba da Kachollom Daju da Malam Shehu Ibrahim da kuma Mary Ogbe.

Kazalika Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya rawaito cewa cikin wadanda suka halacci taron akwai mataimakin shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Farfesa Ibrahim Gambari da kuma Mashawarcin shugaban Kasa kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.

Sauran sune shugabar ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Uwargida Folashade Yemi-Esan da kuma wasu Ministoci takwas (8).

NAN ya kara rawaito cewa an yi shiru na tsawon mintuna domin nuna alhini ga rashin tsohon mamban kwamitin Tonye Graham-Douglas, wanda ya mutu a ranar Talata 25 ga watan Aprilun 2022.

Marigayi Graham-Douglas kafin rasuwarsa ya yi aiki a matsayin Ministan sufurin jiragen sama da kuma ministan Kwadago da nagartar aiki da kuma Ministan yawo bude ido.

Ya rasu ne ranar litinin a wani asibiti mai zaman kansa dake birinin Tarayya Abuja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here