Boko Haram ba ta taɓa zaɓar Buhari a matsayin mai shiga tsakani ba, Jonathan ya yi ƙarya – Garba Shehu

Buhari jonathan

Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya karyata ikirarin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan cewa marigayi shugaba Muhammadu Buhari ya taɓa kasancewa cikin sunayen da Boko Haram ta amince su shiga tsakani a tattaunawa da gwamnatin tarayya.

A cikin wata sanarwa mai zafi a ranar Juma’a, Shehu ya bayyana ikirarin Jonathan a matsayin “ƙarya da siyasa ce kawai,” yana zargin tsohon shugaban ƙasan da yunƙurin sake rubuta tarihi don cimma burin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

“Shehu ya ce: ‘Idan Jonathan na son zama shugaban ƙasa a 2027, ya nemo wani labari ya faɗa wa ‘yan Najeriya. Muhammadu Buhari ba a taɓa zaɓarsa a matsayin mai shiga tsakani ba. Akasin haka ne, Shekau kullum yana zaginsa yana kuma yi masa barazana, kuma tunaninsu sun sha bamban kwata-kwata.’”

Shehu ya tunatar da harin bam da ya auku a Kaduna a 2014 wanda Buhari ya tsira, inda aka zargi Boko Haram da kai harin.

Ya ce yakin neman zaben Buhari ya ta’allaka ne wajen dawo da tsaro da kawar da ta’addanci, ba don wakiltar ajandar Boko Haram ba.

Labari mai alaƙa: Zan mutu da tabon baƙin cikin sace ’yan matan Chibok -Jonathan

A cewar Garba Shehu, rahoton ya samo asali ne daga taron manema labarai a 2012 na wata rukunin Boko Haram ƙarƙashin jagorancin Abu Mohammed Ibn Abdulaziz, wanda ya ce Buhari da wasu dattawan arewa sun dace a matsayin masu shiga tsakani.

Sai dai Abubakar Shekau ya fito da sauri ya karyata wannan batu yana mai cewa Abdulaziz ba shi da wani iko.

Haka kuma, tsohon sakataren yada labarai na CPC, marigayi Rotimi Fashekun, a lokacin ya zargi gwamnatin PDP ta Jonathan da amfani da ikirarin da sunan siyasa, yana cewa dabara ce kawai domin karkatar da hankalin ‘yan Najeriya daga wawurar da ake yi a ƙarƙashin mulkinsu.

Shehu ya yi gargaɗi ga Jonathan da ya guji amfani da ƙagaggun labarai don samun tagomashi a siyasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here