NAPTIP ta ceto mutane 8, tare da kama mutane 2 da ake zargi a Kano

NAPTIP LOGO

Hukumar yaƙi da fataucin Mutane ta ƙasa (NAPTIP) ta bayyana cewa ta ceto mutane takwas da ake zargin za a yi fataucin su tare da cafke wasu mutane biyu da ake zargi a Jihar Kano.

Kwamandan ofishin NAPTIP na shiyyar Kano, Malam Abdullahi Babale, ya bayyana haka a hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a ranar Juma’a a Kano.

Ya ce jami’an hukumar sun tare wadanda abin ya shafa a ranar 1 ga Oktoba a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA).

Babale ya bayyana cewa bincike na farko ya nuna cewa za a kai mutanen zuwa Saudiyya domin bautar da su ta hanyar cin zarafi, inda ake zargin wasu ‘yan asalin kasar Ghana biyu da kasancewa cikin gungun masu fataucin mutanen.

Ya ce mutane shida daga cikin wadanda aka ceto na tafiya ne da tikitin jirgi na hanya daya kacal zuwa Saudiyya, sannan aka kama daya daga cikin wadanda ake zargin, yayin da dayan ya tsere.

Kwamandan ya ce wadanda aka ceto mata ne masu shekaru tsakanin 18 zuwa 43, daga jihohin Kano, Katsina, Bauchi da Kaduna.

Haka kuma hukumar ta ceto wasu mata biyu da aka yi fataucin su zuwa kasar Burkina Faso daga Kano a ranar 24 ga Yuli, 2025 domin cin zarafin su ta hanyar yin fasiƙanci.

A cewar Babale, an kama wata mace mai shekara 30 a Kano da ake zargi da hannu a cikin lamarin, sai dai bincike ya nuna cewa ta yi amfani da hanyar Legas wajen tura wadannan mata zuwa wurin ‘yar uwarta da ke zaune a Burkina Faso.

Ya ce an dawo da wadannan mata daga Burkina Faso ta hanyar kasa, bayan an cafke wadda ake zargi.

Babale ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargi a kotu bayan kammala bincike.

Ya kuma ce, wadanda abin ya shafa za su samu shawarwari da kulawa na musamman kafin a mayar da su ga iyalansu, bisa tsarin hukumar na kula da wadanda aka yi fatauci.

Kwamandan ya yi kira ga iyaye da su kasance masu lura da ‘ya’yansu, tare da yin taka-tsantsan wajen kare su daga masu fatauci, wadanda kan yi amfani da matsin tattalin arziki wajen jan hankalin mutane da alkawuran bogi na rayuwa mai kyau a kasashen waje.

Haka kuma ya bukaci jama’a da su rika sanar da hukumomi duk wani motsi ko al’amari da ya shafi fataucin mutane.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here