Kirsimeti: Akalla mutum 22 sun jikata biyo bayan hadarin mota a Gombe

Gombe accident 459x430

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, ASP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da cewa mutane 22 sun jikkata bayan wata mota ta kutsa cikin jerin gwanon mabiya addinin Kirista a Tumfure, kusa da Gombe, a ranar Laraba.

ASP Abdullahi ya ce ba a samu asarar rai ba, kuma wadanda suka jikkata suna samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) da Asibitin Kwararru na Gombe.

Ya bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe biyu na rana yayin da mabiya addinin Kirista suke kan hanyar zuwa Fadar Mai Martaba da Gidan Gwamnati, tare da rakiyar ‘yan sanda, sai wata mota kirar Sharon mai dauke da buhunan shinkafa ta rasa birki ta kutsa cikin jerin.

Mota ta kone sakamakon harin fusatattun matasa, yayin da direban ya gudu. ⁰Kwamandan ‘yan sanda ya ce ana ci gaba da kokarin gano direban.

Shugaban jerin gwanon, Mista Shamsuddeen Kachalla, ya ce mutane fiye da 40 ne suka jikkata, inda aka kwashe 12 zuwa FTH, yayin da 28 ke jinya a Asibitin Kwararru.

Gwamna Inuwa Yahaya ya jaje wa wadanda abin ya shafa, yana mai kira ga matasa da su zauna lafiya. Hakanan ya bukaci mabiya addinin Kirista su zauna lafiya da makwabtansu Musulmai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here