Bankin Polaris ya nada Ahmad a matsayin sabon Shugaba, Sonola Manajan Darakta

Polaris Bank
Polaris Bank

Bankin Polaris ya nada sabon kwamitin gudanarwar bankin wanda zai jagoranci garawa da bunkasar bankin.

Shugaban bankin Polaris Alhaji Muhammad Ahmad ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Legas.

Sanarwar ta ce hukumar ta samar da wasu daraktoci shida da ba na zartarwa ba da kuma manyan daraktoci uku masu zartarwa.

Sabbin ‘yan kwamitocin bankin sun hada da: Shi kan sa Ahmad a matsayin shugaba; Abubakar Suleiman, Ahmed Almustapha da Salma Mohammed a matsayin daraktoci mara sa zartarwa; Adeleke Adedipe, Daraktan zartarwa.

Sauran sune Francesco Cuzzocrea, Olabisi Odunowo a matsayin daraktoci mara sa zartarwa; Abdullahi Mohammed da Segun Opeke a matsayin manyan daraktocin zartarwa.

Haka kuma sanarwar ta bayyana Adekunle Sonola, tsohon babban darakta a bankin Union, a matsayin sabon Manajan Darakta kuma babban jami’in gudanarwa na cibiyar hada-hadar kudi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rawaito cewa an samu sauyin mallakar bankin ne bayan da babban bankin Najeriya ya sanar da kammala yarjejeniyar siyar da hannun jarin bankin 100 bisa 100 na hannun jarin bankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here