A ranar Lahadi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu domin halartar taron duniya na farko na 2022.
A cikin wata sanarwa da Femi Adesina ya sanyawa hannu, yace gwamnatin kasar Koriya ta Arewa da hukumar lafiya ta duniya ne suka shirya gangamin taron.
“An gayyaci Najeriya zuwa taron ne bisa zabin da ta yi da wasu kasashen Afirka biyar da hukumar lafiya ta duniya da kungiyar Tarayyar Turai suka yi a yayin taron karshe na kungiyar tarayyar turai da Afirka a Brussels na kasar Belgium a watan Fabrairun bana.
“Shugaba Buhari wanda ake sa ran zai gabatar da jawabi a wajen taron, kuma zai gana da shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol, zai kuma nemi wasu hanyoyin hadin gwiwa da ka iya yin tasiri ga rayuwa da lafiyar ‘yan Najeriya.
“Ana saran cikin ‘yan rakiyar da zasuyi bulaguron da shugabanan akwai: Gwamna Aminu Masari da Abubakar Bello na jihohin Katsina da Neja; Geoffrey Onyeama, Osagie Ehanire da Adeniyi Adebayo, ministocin harkokin waje, kiwon lafiya, masana’antu, kasuwanci da zuba jari; da Timipre Sylva, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur.
“Sauran ‘yan tawagar su ne: Maj-Gen. Mohammed Monguno (mai ritaya), mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro; Amb. Ahmed Abubakar, Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa da sauran su.
Ana sa ran shugaba Buhari zai dawo gida bayan kammala taron.












































