Ya ce: “Za mu horas da Jami’an Duba-aikin Manyan Turawan Zabe kimanin 17,685 da Manyan Turawan Zabe wato Presiding Officers da Mataimakan Manyan Turawan Zabe (Assistants Presiding Officers) 707,384; sai Jami’an Tattara Sakamako (Collation Officers) 11,083; da Kwararrun Jami’ai (Registration Area Technical Officers) kimanin 12,991 da Jami’an Tsaro kimanin 20,000 da Manajojin kula da Cibiyoyin Zabe (Registration Area Centres Managers) 6,009 .”
A cewar Babban Daraktan za a gudanar da tarukan horas da jami’an zaben ne da cikakken kudurin tabbatar da yin zabe mai ‘yanci kuma cikin gaskiya da adalci a 2023.
Sa’ad Idris ya ce cibiyarsu ta dukufa wajen sauke nauyinta na tabbatar da ganin dukkan ma’aikatan wucin gadin sun samu ingantaccen horo kuma mai aminci.