APC: Abubakar Kyari Ya Maye Gurbin Abdullahi Adamu

Senator Abubakar Kyari
Senator Abubakar Kyari

Muƙaddashin shugaban APC na ƙasa shiyyar Arewacin Najeriya, Sanata Abubakar Kyari ya zamo shugaban riƙon ƙwaryar jam’iyyar.

Hakan ya biyo bayan murabus  da shugaban jam’iyyar  Sanata Abdullahi Adamu ya yi.

Kundin tsarin mulkin jam’iyyar ne ya bai wa muƙaddashin shugaba daga shiyyar da  shugaban da ya yi murabus ya fito ya ɗare kujerar na wucin-gadi.

Sanata Kyari ya jagoranci wasu jiga-jigan APC wurin gudanar da taron gaggawa da ranar Litinin a Abuja.

Waɗanda suka halarci taron su ne Muƙaddashin shugaba shiyyar kudancin Najeriya: Emma Enukwu, Mataimakin shugaba  shiyyar Arewa maso Yamma: Salihu Lukman, Mataimakin shugaba shiyyar Arewa maso Gabas: Salihu Mustapha da  Mataimakin shugaba shiyyar Arewa ta Tsakiya: Muazu Bawa.

Sauran su ne Mataimakin shugaba shiyyar Kudu maso Yamma: Isaacs Kekemeke, Mataimakin shugaba shiyyar Kudu maso Gabas, Ejoroma Arodiogu da Muƙaddashin sakataren jam’iyyar na ƙasa: Barista Festus Fuanter.

Sanata Abubakar Kyari, ɗa ne ga tsohon kantoman mulkin soji na jihar Arewa ta tsakiya daga 1967 zuwa 1975 Burgediya Abba Kyari.

An haife shi ranar 15 ga Janairun 1960 a jihar Borno.

Ya samu digirn farko daga jam’iar Tennessee dake Amurka a 1986, kuma ya yi digiri na biyu a jami’ar Webster dake Missouri, Amurka a 1989.

A 1998 aka zaɓe shi ɗan Majalisar Wakilai ƙarƙashin tutar jam’iyyar UNCP.

Haka kuma an sake zaɓensa a 1999 ƙarƙashin jam’iyyar ANPP.

Ya yi kwamishina a jihar Borno daga 2003 zuwa 2005 da kuma 2007 zuwa 2011.

A 2015 aka zaɓe shi sanata mai wakiltar Borno ta Tsakiya ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Sanata Kyari ya sake lashe zaɓe a 2019 kuma ya na kan kujerar ne aka naɗa shi Muƙaddashin shugaban APC na ƙasa a 2022.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here