Kungiyar Manchester United ta kara fadawa cikin halin ƙunci bayan ta sha kashi da ci 3-1 a hannun Brentford a filin Gtech Community Stadium a ranar Asabar, lamarin da ya ƙara matsa wa mai horas da su, Ruben Amorim, lamba.
Dan wasan gaba na Brazil, Igor Thiago, ya taka rawar gani inda ya zura ƙwallaye biyu a cikin mintuna 20 na farko.
Ya fara cin kwallo a minti na 8, bayan ya guje wa tarkon daga baya, sannan ya doke mai tsaron ragar United, Altay Bayindir, cikin natsuwa.
A minti na 20, Thiago ya kara kwallo ta biyu bayan ya buga daga kwallon da ta dawo daga raga.
United ta dawo cikin wasan a minti na 26 lokacin da Benjamin Šeško ya ci kwallo bayan ɗan ruɗani a cikin akwatin Brentford.
Sai dai burin United ya dusashe a minti na 71 lokacin da aka basu bugun fanareti bayan an yi wa Bryan Mbeumo katsalandan.
Amma kyaftin ɗin United, Bruno Fernandes, ya kasa cin kwallon, domin mai tsaron ragar Brentford, Caoimhín Kelleher, ya hango inda zai bugi kwallon ya kuma hanashi.
A cikin ƙarin lokaci, Mathias Jensen wanda ya fito daga benci ya kara ci gaba da kunyata United, inda ya kwace kwallon a kai harin bazata, ya kuma jefa ta daga nesa cikin ragar Bayindir, don rufe wasan da ci 3-1.
Wannan nasara ta ba Brentford kwarin gwiwa yayin da suke kallon gaba da fata. Amma ga Manchester United kuwa, mako guda kacal bayan nasarar da suka samu kan Chelsea, sun sake shiga cikin rudani, lamarin da ya sa makomar Ruben Amorim ta kara shiga ruɗani yayin da hutun wasannin kasa-da-kasa ke gabatowa.













































