Gobara ta tashi a shagon siyar da kayan daki na VAVA Furniture da ke kan titin Murtala Muhammad a cikin jihar Kano.
Gobarar ta tashi da misalin karfe 11 na ranar wacce ta dau tsayin lokuci tana ci kafin jami’an kashe gobara su kawo dauki.
Daya daga cikin ma’aikatan shagon, Musa Abubakar ya bayyanawa jaridar Solacebase cewa sun yi kokarin kashe wutar amma abin yafi karfin su.
“Munyi amfani da abin kashi gobara na gaggawa da muke dashi a shagon, amma bamu kai ga kashe wutar ba.”
A dakace mu……