Wata kungiya mai suna “Gov Yahaya Bello Lawyers Volunteer Campaign Forum”, ta yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC da su yi hattara yayin gudanar da al’amuran siyasa don kaucewa yin abin da zai bawa jam’iyyar matsala a zaben 2023 mai zuwa.
A cikin wata sanarwar bayan taro da shugaban kungiyar na kasa Barrista Misis Chilaka Igidi, tare da shugabannin kungiyar shiyoyi shida suka sanyawa hannu, sun yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da umarnin da ya bayar na kwanan kan tabbatar da Gwamna Mai Mala Buni a matsayin shugaban riko na jam’iyyar, kuma shine zai jagoranci babban taron jam’iyyar wanda zai gudana a ranar 26 ga Maris.
Taron ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, bisa tsayawa tsayin daka a kan doka, wajen ganin an magance rigimar da ta kunno kai a cikin jam’iyyar.
Kungiyar ta kuma sha alwashin cewa babu abin da zai hana ta tunkarar kotu idan har shugabannin jam’iyyar APC suka yi wa dokar zabe da kundin tsarin mulkin kasar zagon kasa, idan har aka ci gaba da wannan mumunar lamarin.
An kammala taron ne da yin kira ga jam’iyyar da ta bi tsarin tsarin mulki ta hanyar bai wa duk wani dan Najeriya da ya cancanta dama, ba tare da la’akari da yankin siyasarsa ba.












































