Zargin Zalunci: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Daliban FGC 13

Morufu Tunji Alausa 678x430.jpeg

Gwamnatin tarayya ta dakatar da dalibai 13 na kwalejin gwamnatin tarayya dake jihar Enugu na tsawon makwanni shida bisa zargin cin zarafi a makarantar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa a Abuja ranar Laraba ta hannun daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar, Folashade Boriowo.

Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa ya bayar da umarnin dakatar da daliban bisa wani faifan bidiyo da ya nuna wasu daliban makarantar na cin zarafi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here