’Yan bindiga sun sace mutane 7 a wani sabon hari suka kai a Kano

Kano Map

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai sabon hari a garin Lakwaya da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a jihar Kano, inda suka sace mutane Bakwai a yayin harin.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne a daren Lahadi a ƙauyen Zurin Mahauta da ke yankin Lakwaya, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba da tashin hankali.

Sarkin ƙauyen Zurin Mahauta, Murtala Mai Unguwa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa jami’an tsaro sun gaggauta kai dauki bayan samun rahoton harin, tare da fara bin sawun masu garkuwa da mutanen domin ceto waɗanda aka sace da kuma kama masu laifin.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wasu al’ummomi a ƙananan hukumomin Tsanyawa da Shanono a jihar Kano sun sha fuskantar hare-haren ’yan bindiga a baya-bayan nan, inda aka sace sama da mutane 20 a lokuta daban-daban.

A martani kan lamarin, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojin Brigade ta uku, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya bayyana cewa an sace mutane biyar, kuma dakarun soji sun riga sun fara bin diddigin ’yan bindigar domin ceto waɗanda abin ya shafa.

A baya bayan nan Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyara wasu daga cikin al’ummomin da harin ya shafa a makon da ya gabata, inda ya tabbatar wa mazauna yankunan cewa gwamnati za ta ci gaba da ba su cikakken goyon baya wajen magance matsalar tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here