Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta ce ta kama Mista Christopher Oluchukwu, tsohon kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) bisa hannu a badakalar ayyukan yi.
A karar da ICPC ta shigar a babbar kotun jihar Katsina 3, an zargi wanda ake tuhuma da karbar kudi Naira Dubu 200,000 da Naira Dubu 300,000 da kuma Naira Dubu 400,000 daga hannun wasu mutane uku bisa zargin samawa ‘ya’yansu ayyukan yi na NSCDC.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mukaddashin daraktan hukumar ICPC, Demola Bakare, ta fitar a ranar Alhamis.
Karin labari: Shin ko kun san waye ministan cikin gida a Najeriya, to ku karanta wannan labarin
Ta ce wadanda abin ya shafa sun kai rahoton lamarin ga ICPC bayan wanda aka yankewa hukuncin ya kasa samun aikin da aka ce ya ki mayar da kudadensu.
Ta ce a yayin zaman kotun, lauyan ICPC, Ibrahim Garba, a kan tuhume-tuhume 9, ya shaida wa kotun yadda matakin da wanda ake tuhuma yayi ya sabawa sashe na 8 da 10 da 19 na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaka na shekarar 2000.
A hukuncin da ya yanke a ranar Talata, Mai shari’a Abbas Bawale ya samu Oluchukwu da laifukan tuhume-tuhume tara tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da zabin tara ba.