Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta Kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta shekarar 2024, inda dalibai 57,114 suka samu maki biyar ko sama da haka a cikin Harshen Ingilishi da Lissafi, wanda ke wakiltar kashi 67.35%.
Adadin wadanda suka yi rajista ya kai 86,067 tare da jimillar darussa 29 da aka yi nazari a kansu.
NECO ta bayyana hakan a ranar Juma’a cewa jimillar mutane 84,799 ne suka zana jarabawar.
Karin karatuJami’ar KWARA ta yi martani kan dakatarwar ilimin shari’a da JAMB tayi
Dalibai 70,711 da ke wakiltar 83.39% sun sami maki biyar da sama da haka ba tare da sun samu darussan Ingilishi da lissafi ba.
NECO ta kara da cewa an kama dalibai 6,160 tare da rubuta sunan su sakamakon satar amsa, yayin da masu sanya ido a jarrabawar su 7 su ma aka sanya sunayen su musamman a jihohin Oyo, Ogun, Legas, Ebonyi da Cross Rivers saboda taimakawa wajen aikata laifin satar jarrabawa.