Tinubu ya sauka a Ethiopia don halartar taron AU

Tinubu depart US 750x430

Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa birnin Adis Ababa na kasar Ethiopia domin halartar zaman taro na 38 na shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afrika AU.

Shugaban ya samu tarba a filin tashi da saukar jiragen sama na Eshetu Legesse, kuma ya samu tarba daga mataimakin shugaban kula da harkokin kasa Ambasada Yusuf Tuggar, Ministan Harkokin Waje, da Amb.Nasir Aminu, mai kula da ofishin jakadancin Najeriya a Ethiopia.

Daga baya Tuggar ya yi wa shugaba Tinubu bayani kan taron da wasu nasarorin diflomasiyya da kasar ta samu, zaman da ya gudana har zuwa misalin karfe 2 na safiyar ranar Juma’a, kamar yadda Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Karin karatu: Tinubu zai tafi Faransa, gabanin tafiyarsa Addis Ababa

Daga cikin nasarorin har da sake zaben Amb. Bankole Adeoye a matsayin kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka.

A wajen taron akwai Mista Wale Edun, ministan kudi Abubakar Badaru, Ministan Tsaro; Jumoke Oduwole, Ministan Kasuwanci da Zuba Jari; Festus Keyamo, ministan sufurin jiragen sama da Muhammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa.

Balarabe Abbas Lawal, Ministan Muhalli da Doris Uzoka-Anite, Karamin Ministan Kudi, sai Amb. Mohammed Mohammed, Darakta-Janar na hukumar leken asiri ta kasa, da Vice Admiral Emmanuel Ogalla, babban hafsan sojin ruwa, suma sun halarci taron.

Taron na AU na bana, mai taken “Adalci ga ‘yan Afirka da mutanen Afirka ta hanyar ramuwar gayya,” ya mai da hankali kan adalcin gyara da kuma warkar da wariyar launin fata.

Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi a taron matakin koli na kwamitin sulhu da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka, inda za a tattauna kan kalubalen tsaro da nahiyar ke fuskanta a halin yanzu, ciki har da karuwar tashe-tashen hankula a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.

Shugaban kasar zai halarci taruka kan kudaden kiwon lafiya, da kafa hukumar bada lamuni ta Afirka, da sauyin yanayi.

Shugaba Tinubu zai koma Abuja ranar Litinin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here